Isa ga babban shafi

Jami'an agaji na ci gaba da laluben wadanda gini ya danne bayan harin Somalia

Jami’an agaji na ci gaba da aikin laluben gawarwaki a karkashin baraguzan gine-ginen da bama-bamai suka tarwatsa bayan harin kunar bakin waken jiya Asabar da ya kashe gomman mutane a Somalia.

Wani yanki da 'yan ta'adda suka kai hari a Somalia.
Wani yanki da 'yan ta'adda suka kai hari a Somalia. AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Alkaluman mutanen da suka mutu a harin kunar bakin wajen na jiya Asabar a birnin Beledweyne na ci gaba da karuwa duk da cewa har zuwa yanzu mahukuntan kasar ba su sauya alkaluman daga mutum 13 da suka sanar a jiyan ba.

Tun farko, wata babbar mota ce makare da bom ta tarwatse a gab da wani dogon gini da ke dauke da tarin ma’aikata, lamarin da nan take ya hallaka mutum 13 yayinda ginin ya danne wasu da dama.

Zuwa yanzu dai akwai mutane 45 da ke karbar kulawar gaggawa a asibitoci yayinda wasu da dama suka yi batan dabo bayan faruwar harin na kunar bakin wake.

Babban kwamandan ‘yan sandan yankin na Beledweyne Sayid Ali ya bayyana cewa, alkaluman wadanda harin ya hallaka za su iya karuwa lura da yadda ake da tarin mutanen da baraguzan gine-gine suka danne.

Tuni dai shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya aike da sakon ta’aziyya ga wadanda harin na jiya Asaba rya rutsa da su tare da saka nanata alwashinsa na kawo karshen ta’addancin kungiyar Al-Shabaab.

A cewar shugaban akwai fatan makamancin harin ba zai sake faruwa a kowanne yanki na Somalia ba, lura da sabuwar damarar da suka daura ta kawo karshen mayakan na Al-Shabaab.

Fiye da shekaru 15 dakarun Somalia suka shafe suna yaki da mayakan kungiyar ta Al-Shabaab da ke ci gaba da kai muggan hare-hare sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.