Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta tilasta jiragen kasan Birtaniya dakatar da aiki

Kamfanin Jiragen Kasan Eurostar dake Birtaniya ya sanar da dakatar da gomman jiragen kasansa dake safara tsakanin Birtaniya da sauran sassan Turai, saboda matsalar ambaliyar ruwa da aka samu a layukan dogo na karkashin kasa kusa da birnin Landan da kuma kudancin Kasar.

Wani Jirgin Eurostar
Wani Jirgin Eurostar © Reuters/Pascal Rossignol
Talla

Da farko dai jiragen kasan Eurostar 14 ne aka soke ayyukan nasu, daga bisani kamfanin ya sanar da dakatar da dukkanin jiragen kasan kasar 41 da suka yi shirin yin aiki a asabar dinnan, la’akari da yadda matsalar ambaliyar ke ci gaba da tsananta.

Haka ma tun farko ba a gane dalilin da ya haifar da ambaliyar ba a layukan dogo na karkashin kasa dake kogin Thames kusa da Ebbsfleet dake kudancin birnin Landan.

A ‘yan kwanankin nan wasu daga cikin sassan Birtaniya suka yi fama da saukar mamakon ruwan sama, wadda ta tilasta hukumomi aika sakon gargadi na yiwuwar fuskantar guguwa mai karfi a kudancin Kasar.

Dubban mutane da suka makale a tashar jirgin kasan Eurostar dake Birtaniya
Dubban mutane da suka makale a tashar jirgin kasan Eurostar dake Birtaniya REUTERS - BELINDA JIAO

Matsalar dakatar da aikin jiragen kasan kasar na zuwa ne daidai lokacin da ake gab da shiga sabuwar shekara ta 2024, abinda ya yi sanadiyar makalewar dubban fasinjoji.

Kafofin talabijin na Kasar sun yi ta wallafa hotunan bidiyon yadda ruwa ke shiga wani layin dogo na karkashin kasa, abin ke kara tabbatar da amfanin dakatar da ayyukan jiragen kasan.

A dayan bangaren, Hukumar hasashen yanayi na Kasar ta kuma yi gargadin samun saukar ruwan sama da kankara a sassan Kasar ta Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.