Isa ga babban shafi

Shugaban China na ziyara a Faransa domin tattaunawa kan rikicin Ukraine da Rasha

Shugaba Xi Jinping ya yabawa dangantakar da ke tsakanin kasar China da Faransa a matsayin abin koyi na a fadin duniya.

Shugaban China Xi Jinping  kenan tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris.
Shugaban China Xi Jinping kenan tare da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a birnin Paris. AP - Thibault Camus
Talla

Xi ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai birnin Paris jiya Lahadi, dangane da takaddamar cinikayya da ke ci gaba da karuwa tsakanin China da kungiyar Tarayyar Turai.

Tun gabanin ziyarar, an yi tsammanin shugaban Faransa Emmanuel Macron, zai bukaci Xi da ya samar da daidaito a harkokin kasuwanci da kuma amfani da tasirinsa ga Rasha kan yakin Ukraine.

Sai dai masu sharhi na ganin ko da Macron din ya gabatar da bukatar ta sa, ba lallai burinsa ya cika cikin sauki ba.

Ziyarar ta Xi na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da takaddamar kasuwanci tsakanin Tarayyar Turai da China.

Ita dai Faransa na goyon bayan wani binciken da Tarayyar Turai ta gudanar kan fitar da motoci masu amfani da lantarki da China ke yi, yayin da a watan Janairu kuma, Beijing ta bude wani bincike kan shiga da kayayyaki Faransa, matakin da ake kallonsa a matsayin ramuwar gayya ga binciken Tarayyar Turan.

A yau Litinin ne ake sa ran shugaban na China zai gana da Macron da kuma shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.