Matakan da Jihar Katsina ke dauka don dakile tasirin ambaliyar ruwa a bana
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:25
A duk shekara, ambaliyar ruwa na yin sanadin mutuwar mutane da janyo hasarar dukiya mai tarin yawa a Najeriya, duk kuwa da fadakarwar da hukumomi kan yi don kaucewa faruwar hakan.
Jahar Katsina na daga cikin jihohin da ke fuskantar wannan matsala, domin ko a farkon daminar bana sai da kimanin mutane 10 suka rasa rayukansu, tare da lalata gidaje sama da dari biyu.
Dangane da irin matakan da gwamnatin jihar ta Katsina ke dauka don kare sake faruwar hakan da kuma irin gudunmuwar da ta bai wa wadanda iftila’in ya shafa, Khamis Saleh ya tattauna da shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Hajiya Binta Dangani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu