Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Amir Muhammad Harbo kan yadda ambaliyar ruwa ke barna a masarautar Hadeja

Wallafawa ranar:

Rahotanni daga Najeriya sun ce ruwan saman da ake ci gaba da shatatawa ya haifar da mummunar ambaliya a karin kananan hukumomi guda 8 dake yankin Hadejia, yayin da gwamnatin Jihar tace mutane 92 ne suka rasa rayukansu yanzu haka.

Manomi Ali Dan Ladi tsaye cikin gonar sa da ambaliyar ta lalata a yankin masarautar Rimgim dake jihar Jigawa mai makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya.
Manomi Ali Dan Ladi tsaye cikin gonar sa da ambaliyar ta lalata a yankin masarautar Rimgim dake jihar Jigawa mai makwaftaka da jihar Kano a arewacin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Mazauna wadannan yankunan dai na cikin mummunan yanayi, inda suke bukatar agajin gaggawa, yayin da ruwan ya katse wasu daga cikin hanyoyin yankin.

Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Amir Muhammad Harbo, daya daga cikin matasan dake aikin taimakawa wadanda iftila’in ta afkawa, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.