Matsayin kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya kan haramta kiwo a kudancin kasar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:26
Kungiyar Dattawan Arewacin Nigeria ta ce ba ta adawa da duk wani kyakkyawan tsari da gwamnati za ta bijiro dashi don kyautata sha‘anin kiwo da makiyaya Fulani ke yi domin tafiya daidai da zamani.
Sai dai kungiyar ba ta goyon bayan muzgunawa Fulanin makiyaya da sunan haramta musu kiwo.
A kwanakin baya ne dai Gwamnonin jihohin kudancin Nigeria 17 suka gabatar da bukatar hana kiwo a jihohinsu, bayan wani taro da suka yi a garin Asaba na jihar Delta.
Kan wannan batu Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Dakta Hakeem Baba-Ahmed kakakin kungiyar Dattawan na Arewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu