Isa ga babban shafi

Tankokin yakin Isra'ila sun sake kutsawa arewacin Zirin Gaza

Tankokin yaƙin Isra’ila sun sake kutsawa arewacin Zirin Gaza a jiya Talata, yankin da suka janye daga cikinsa a makwannin da suka gabata.

Daya daga cikin tankokin yakin Isra'ila a arewacin Zirin Gaza.
Daya daga cikin tankokin yakin Isra'ila a arewacin Zirin Gaza. REUTERS - RONEN ZVULUN
Talla

Jiragen yaƙin Isra’ilar sun kuma yi ruwan wuta ta sama kan Rafah, gari na ƙarshe a kudancin Zirin Gaza da Falasɗinawa ke samun mafaka, lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu.

Falasɗinawan da suka rage a arewacin Gaza sun ce tankokin yaƙin Isra’ila sun yi wa makarantu da dama ƙawanya, inda fararen hular da suka rasa muhallansu ke samun mafaka.

Yayin da dakarun Isra'ila suka cigaba da kai hare-hare a Gaza, wani lokaci a wannan Laraba ake sa ran majalisar ƙolin kasar za ta sake zama karo na uku domin tattaunawa kan irin martanin da ya dace ta maida wa Iran, biyo bayan jerin hare-haren da ta kai mata da makamai masu linzami sama da 300 a ƙarshen makon da ya gabata, don daukar  fansar harin Isra’ilar da ya kashe mata sojoji a ofishin jakadancinta da ke Syria.

Sake zaman majalisar sojin Isra’ilar na zuwa ne bayan da Amurka ta ce muddin ta kuskura ta kai  wa Iran farmaki, to fa ita kaɗai za ta fafata yaƙin da ta ballo, domin babu ruwanta.

Tuni dai babban hafsan sojin Isra’ila Herzi Halevi ya  bayyana cewa ba shakka za su maida wa Iran martani, sai dai bai bayyan lokaci da kuma girman matakin da za su ɗauka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.