Isa ga babban shafi

Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani kan harin da Iran ta kai mata

Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani kan Iran, bayan harin ramuwar gayyar da ta kai mata makon da ya gabata. Sai dai ba ta bayyana lokaci da kuma girman irin matakin ramuwar da za ta dauka ba.

Shugaban sojojin Isra'ila Laftanar Janar Herzi Halevi daga ɓangaren dama.
Shugaban sojojin Isra'ila Laftanar Janar Herzi Halevi daga ɓangaren dama. AFP - -
Talla

Babban hafsan sojin Isra'ila Herzi Halevi, ne ya shaidawa dakarun sojin kasar hakan yana mai cewa babu gudu ba ja baya sai an mayar da martani ga harin da Iran ta kai kan kasar.

Sai dai Iran ta mayar da martanin cewa ba ta da burin ganin ɓarkewar yaƙi tsakaninta da Isa'ila, amma fa duk ƙasar da ta lakuci hancinta da za ta ɗanɗana kuɗarta.

A can Zirin Gaza kuwa, jiya Litinin likitoci suka sake gano wani makeken ƙabari a Al-Shifa asibiti mafi girma a yankin na Gaza, wanda sojojin Isra'ila suka shafe makwanni biyu suna yi wa ƙawanya gami kai samame cikinsa.

Yanzu haka dai likitocin sun tabbatar da gano gawarwakin mutum 10 a cikin makeken ƙabarin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wani wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa kimanin kashi 90 cikin 100 na gine-gine kusan dubu 4,000 da ke kan iyakar yankin gabashin Gaza, Isra'ila ta ruguza yayin hare-haren da take kai wa da sunan murkushe mayakan Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.