Isa ga babban shafi

Zaman dar-dar ya karu a Gabas ta Tsakiya saboda barazanar Iran kan Isra'ila

Kamfanin Jiragen saman Jamus na Lufthansa, ya tasawaita matakinsa na kauracewa jigila zuwa birnin Tehran, saboda zaman dar-dar din da ake ciki a Yankin Gabas ta Tsakiya, inda ake fargabar cewa kowane lokaci daga yanzu, Iran na iya kai harin ramuwar gayya don mayar da martani kan farmakin da Isra’ila ta kai wa ofishin jakadancinta a Syria.

Ayatollah Ali Khamenei
Ayatollah Ali Khamenei © Wana News agency / Reuters
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar, kamfanin jiragen saman na Lufthansa da ya saba kai komo zuwa Tehran sau shida a mako ya ce ya tsawaita jigilar fasinjoji zuwa babban birnin na Iran ne har zuwa ranar 13  ga watan Afrilu.

A baya bayan nan ne dai wani Kamfanin Dillancin Labaran Iran a shafinsa na X, ya wallafa rahoton cewa an rufe ilahirin sararin samaniyar kasar domin bai wa sojoji damar atasaye. Sai dai jim kadan bayan hakan kamfannin dillancin labaran ya sauke rahoton daga shafin nasa gami da musanta cewar ya taba wallafa makamancinsa.

Tun ranar 1 ga watan Afrilu zaman dar dar ya karu a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da Amurka ke cikin shirin ko ta kwana dangane da shirin Iran na mayar da martani kan ragargaza ofishin jakadancinta da jiragen yakin Isra’ila suka a Syria, inda suka kashe mata dakarun juyin juya hali 7, cikinsu har da babban kwamanda guda.

A ranar Larabar nan, jagoran juyin juya halin na kasar Iran Aayatollah Ali Khamenei ya ce ya zama dole su hukunta Isra’ila, kuma za su cika alwashin da suka dauka.

Har yanzu dai Isra’ilar ba ta tabbatar da cewa ita ce ta kai hari kan ofishin jakadancin na Iran a Syria ba, sai dai ma’aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.