Isa ga babban shafi

Shugabannin Gabas ta Tsakiya sun cacaki Isra'ila a kan yadda take ragargazar Gaza

Duniya – Shugabannin kasashen Larabawa da Iran sun bayyana matukar bacin ransu dangane da matakan da Isra’ila ke dauka a yakin da take fafatawa da Hamas a Gaza, yayin da ake fargabar cewar yakin na iya fadada wajen janyo wasu kasashe su sanya hannu a ciki.

Yarima Muhammad bin Salman na Saudi Arabia da Firaminsitan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Yarima Muhammad bin Salman na Saudi Arabia da Firaminsitan Isra'ila Benjamin Netanyahu © Yonatan Sindel/Flash90; Bandar Aljaloud/Saudi Royal Palace via AP
Talla

Taron gaggawar da ya samu halartar shugabannin kasashen Larabawa da kuma na kasashen Musulmi da ake kira OIC, na zuwa ne bayan harin da kungiyar Hamas ta kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane kusan 1,200, akasarin su fararen hula tare da garkuwa da wasu 239.

Bayan haka, Isra’ila ta kaddamar da munanan hare haren da suka yi sanadiyar hallaka Falasdinawa sama da dubu 11, akasarin su fararen hula da kuma kananan yara, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Hamas ta sanar.

Shugaban Iran  Ebrahim Raïssi a kasar Saudiyya
Shugaban Iran Ebrahim Raïssi a kasar Saudiyya via REUTERS - WANA NEWS AGENCY

Mai masaukin baki Saudiya ta hannun Yarima Muhammad bin Salman ta zargi Isra’ila da alhakin kashe jama’ar Falasdinawa a yakin dake ci gaba da daukar hankalin kasashen duniya.

Salman yace suna da yakinin cewar babu abinda zai tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin da ya wuce kawo karshen mamayar da Isra’ila ta yi da kuma gine ginen da take yi a yankunan Falasdinawa dake Gaza da Gabar Yamma da kogin Jordan.

Taron shugabannin kasashen Larabawa da na kasashen Musulmi na OIC
Taron shugabannin kasashen Larabawa da na kasashen Musulmi na OIC © Saudi Gazzete

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi, a ziyarar sa ta farko da ya kai Saudiya tun bayan mayar da huldar da kasashen biyu suka yi a watan Maris, ya bukaci kasashen Musulmi da su bayyana sojojin Isra’ila a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda saboda abinda suka yi a Gaza.

Ita dai Isra’ila tace bukatar ta itace murkushe kungiyar Hamas, yayin da ta zarge ta da sanadiyar hallaka Falasdinawan da suka mutu saboda yadda take amfani da su a matsayin garkuwa, zargin da Hamas ta yi watsi da shi.

Yadda Falasdinawa mazauna Gaza ke ficewa daga yankin
Yadda Falasdinawa mazauna Gaza ke ficewa daga yankin © AP/Fatima Shbair

Da dai an shirya taron kasashen Larabawar da na Kasashen Musulmi mai wakilai 57 ne daban daban, amma rashin cimma matsaya a tsakanin wakilan kasashen Larabawa ya sa aka hade tarukan biyu.

Wasu daga cikin kasashen da suka halarci taron, irin su Algeria da Lebanon, sun bukaci daukar matsayi mai karfi a kan yadda aka ragargaza Gaza, ta hanyar katse man fetur da ake kaiwa Isra’ila da kawayenta da kuma katse huldar diflomasiya da kuma na kasuwancin da wasu kasashen Larabawa ke da shi da kasar.

Shugabannin da suka halarci taron Saudiya
Shugabannin da suka halarci taron Saudiya © Saudi Gazzete

Rahotanni sun ce akalla kasashe 3 da suka hada da Daular Larabawa da Bahrain da suka mayar da huldar diflomasiya da Isra’ila a shekarar 2020, sun ki amincewa da bukatar, kamar yadda wasu majiyoyin diflomasiya suka shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Kafin dai gudanar da taron, kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu, tace bata fatan ganin wani abin kirki ya fito daga taron, saboda yadda shugabannin Larabawa suka yi jinkiri wajen daukar mataki.

Majinyata da wadanda suka rasa matsugunin su a asibitin Al-Shifa dake Gaza
Majinyata da wadanda suka rasa matsugunin su a asibitin Al-Shifa dake Gaza AFP - KHADER AL ZANOUN

Mohammed al-Hindi, mataimakin Sakatare Janar na kungiyar ya shaidawa manema labarai a Beirut cewar, basa sanya makomar su a kan irin wadannan tarurruka.

Isra’ila da babbar kawarta Amurka dake goyan bayan yakin, sun ki amincewa da duk wata bukata ta tsagaita wuta, abinda ya gamu da mummunar suka a wajen taron.

Shugaban Iran Raisi yace Amurka ta hana tsagaita wuta a Gaza, matakin dake barazanar fadada yanayin yakin.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan yace abin kunya ne ganin yadda kasashen yammacin duniya ke daga murya su wajen kare hakkin Bil Adama da kare ‘yancin jama’a, amma suka yi shiru a lokacin da ake yiwa Falasdinawa kisan kiyashi.

Shi kuwa shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas yace Amurka ke da karfin fada aji a kan Isra’ila, kuma itace ke da alhakin rashin samun maslaha ta fuskar siyasa domin warware matsalar.

Daga cikin mahalarta taron na Riyadh harda shugaban Masar, Abdel Fatah al Sisi da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim Al-Thani da shugaban Syria Bashar al Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.