Isa ga babban shafi

Rikicin Isra'ila da Hamas na kara bazuwa a Gabas ta Tsakiya

Ma’aikatar kula da lafiyar yankin Gaza ta ce a cikin sa’oi 24 da suka gabata, hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa 266 ciki kuwa harda yara 117.

Yadda Falasdinawa ke ci gaba da laluben 'yan uwansu a karkashin burabuzai, bayan wani hari da Isra'ila ta kai.
Yadda Falasdinawa ke ci gaba da laluben 'yan uwansu a karkashin burabuzai, bayan wani hari da Isra'ila ta kai. AP - Hatem Ali
Talla

Akwai barazanar wannan yaki na Isra'ila da Hamas ya karade yankin gabas ta tsakiya, bayan da Amurka ta aike da karin makamai ga Isra'ila.

Isra’ila ta kai wasu hare-hare birnin Damascus da kuma tashar jiragen sama da ke Aleppo a ranar lahadin nan, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar ma’aikata biyu da kuma dakatar da aiki a cikinsa.

Haka nan an gwaba wani mummunar rikici tsakanin mayakan Hizbollah da ke samun goyon bayan Iran da sojojin Isra’ila a iyakar kasar ta Arewa da Lebanon, inda aka kashewa mayakan Hizbollah 4 nan take sannan mutum guda ya rasu daga baya sakamakon raunukan da ya samu.

Majiyar tsaron Lebanon ta ce an kashe mayakan Falasdinawa 11 da fararen hula 4 a iyakarta, sannan ita kuma ma’aikatar tsaron Isra’ila ta tabbatar da kashe mata sojoji 5 da farar hula daya a yankin.

Tun bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban nan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu daya da dari 4, tare da yin garkuwa da wasu dari 212, Isra’ila ta fara ruwan bama-bamai a yankin kudu maso yammacin Gaza.

Wasu daga cikin wuraren da Isra'ila ta kai hari a yankin Gaza.
Wasu daga cikin wuraren da Isra'ila ta kai hari a yankin Gaza. AFP - ZAIN JAAFAR

A cewar ma’aikatar kulada lafiyar Gaza, izuwa lahadin nan Falasdinawa dubu 4 da dari 741 suka rasa rayukansu, wasu dubu 15 da dari 898 suka samu raunuka, yayinda wasu sama da miliyan daya ke dauke da kananan raunuka.

Sakataren harkokin tsaron Amurka Lloyd Austin, ya ce Washington za ta ci gaba da aikewa da gudumar kayan yaki ga Isra’ila don karfafa tsaronta.

A nata bangaren, ministan harkokin kasashen wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya gargadi Isra’ila da Amurka da su dakatar da kisan kare dangi da suke yi a yankin Gaza, domin in abin ya ci gaba yankin Gabas ta tsakiya zai shiga cikin wani hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.