Isa ga babban shafi

Amurka ta tsaurara damararta a Gabas ta Tsakiya a matsayin martani ga Iran

Ma’aikatar tsaron Amurka ta dauki matakin karfafa damarar sojinta a Gabas ta Tsakiya a matsayin martani ga abin da ta kira barazanar da Iran da ‘yan kanzaginta ke yi mata a yankin.

Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin.
Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin. REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

Sakartaren tsaron Amurka, Lloyd Austin ya yi umurnin kintsa tsarin tsaron kasar a yankin don ya kasance cikin Shirin ko-ta-kwana, kana ya sanar da karin dakaru cewa ana iya aikewa da su yankin, nan ba da jimawa ba.

Austin bai bayyana yawan dakarun da za a kara a kan wadanda ke girke a yankin na Gabas ta Tsakiya ba.

Wannan matakin na ma’aikatar tsaron Amurka na zuwa ne bayan abin da Austin ya bayyana a matsayin tattaunawa mai tsawo da da ya yi da shugaba Joe Biden.

Matakin, ci gaba ne a kan martanin Biden tun bayan da mayakan Hamas da ke yankin Zirin Gaza suka kai farmaki cikin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka yi garkuwa da mutane kimanin 200 bayan da suka kashe dubu 1 da dari 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.