Israíla ta sha alwashin zafafa hare-hare kan Gaza gabanin shirin kutsawa ta kasa
Rundunar sojin Isra’ila ta ce za ta zafafa ruwan wutar da take yi a Zirin Gaza, wanda ke karkashin ikon kuniyar Hamas, gabanin shirin da ta ke na kutsawa yankin ta kasa, a yayin da hukumomin Majalaisar Dinkin Duniya ke gargadin kazancewar matsalar jinkai a yankin na Falasdinawa.
Wallafawa ranar:
Kashin farko na kayan agaji sun isa wannan yankin da aka wa kawanya daga Masar a jiya Asabar, amma an bayyana manyan motocin dakon kayan, makare da kayan agaji da aka bari su shiga wannan yankin a matsayin digo a cikin teku, duba da bukatun mazauna da suka kai miliyan 2 da dubu dari 3.
Sojin Isra’ila ta yi ta luguden wuta a kan Zirin Gaza a matsayin martani ga harin da mayakan Hamas suka kai kasarta ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane dubu 1 da dari 4.
Hare-haren da Isra’ila ta ke kai wa a matsayin ramuwar gayya ta yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da dubu 4, kamar yadda kungiyar Hamas, wadda ke iko da Zirin Gaza ta sanar.
Wannan lamari ya janyo wa Isra’ila caccaka daga sassan duniya, musamman ma kasashen Larabawa, amma Fira Minista Benjamin Netanyahu ya zake cewa ana kai hare-haren ne a mabuyar mayakan kungiyar Hamas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu