Isa ga babban shafi

Isra’ila na ci gaba da ruwan wuta a kan yankin Zirin Gaza

Kasar Isra’ila na ci gada ba ruwan wuta a kan yankin Zirin Gaza, yayin da aka shiga rana ta 3 na yakin da ake gwabzawa tsakanin ta da Falasdinawa, wanda aka bayyana shi a matsayin mafi muni a shekaru 75 da suke fafatawa. 

Yadda hayaki ke tashi a wasu gine-ginen yankin Falasdinawa bayan hare-haren Isra'ila. 10/10/23
Yadda hayaki ke tashi a wasu gine-ginen yankin Falasdinawa bayan hare-haren Isra'ila. 10/10/23 AP - Hatem Ali
Talla

 

Ya zuwa wannan lokaci an tabbatar da mutuwar Yahudawa sama da 900, yayin da aka kashe Falasdinawa kusan 800, yayin da Majalisar Dinkin Duniya tace akalla Falasdinawa dubu 120 rikicin ya raba da gidajen su. 

Yayin da Israila ta kwashe daren Litinin tana kai munana hare haren sama a kowanne sashe na yankin Gaza, rahotanni na bayyana cewar kungiyar Hamas na ci gaba da bayyana aniyarta na hallaka tarin Yahudawan da ta yi garkuwa da su. 

Sai dai mai magana da yawun kungiyar, Osama Hamdan ya kare kungiyar daga kai hare hare da gangan a kan fararen hula. 

Wasu magoya bayan Hezbollah à Beyrouth, 8/10/23
Wasu magoya bayan Hezbollah à Beyrouth, 8/10/23 © Bilal Hussein / AP

Firamistan israila Benjamin Netanyahu ya bukaci hadin kan bangarorin siyasar kasar sa domin tinkarar yakin, wanda ya ce zai sauya fasalin Gabas ta Tsakiya. 

Yayin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadi dangane da shirin Isra'ilan na yiwa gaza kawanya.

A wannan Laraba ake saran kungiyar kasashen Larabawa ta gudanar da taron a kan yakin, yayin da kasar Masar ke ta kokarin samun amincewar bangarorin domin tsagaita wuta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.