Isra'ila ta kammala yi wa Gaza kawanya bayan kashe Falasdinawa 700
Rundunar Sojin Isra'ila ta sanar da kammala yiwa yankin Gaza kawanya bayan ruwan makaman roka da hare-hare ta sama da ta yiwa yankin daga daren jiya zuwa wayewar safiyar yau, inda ta kwace iko da shingen da Falasdinawa suka karya a ranar Asabar wanda ya raba yankin da cikin Isra'ila.
Wallafawa ranar:
Sanarwar ta rundunar Sojin Isra'ila na zuwa ne a dai dai lokacin da Hamas ke barazanar fara kashe fursunonin da mayakanta suka kamo daga cikin Isra'ila ciki har da mutanen kasashen ketare.
A bangare guda ma'aikatar lafiyar yankin na Gza ta sanar da kisan mutanen da yawansu ya haura 700 a hare-haren na Isra'ila ciki har da wasu 200 a daren jiya kadai.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yara dubu 1 da 300 na sahun mutum dubu 3 da 700 da hare-haren na Isra'ila suka jikkata baya ga wasu tarin kananan yara da mata da kuma dattijai wadanda hare-haren na Sojin Isra'ila ya kashe.
Yanzu dai Isra'ila ta sanar da daukar sabbin sojoji dubu 300 wadanda ta sanya a cikin dakarunta don kaluabalantar hare-haren na Hamas.
Kungiyar kasashen larabawa ta Arab League ta sanar da shirin gudanar da wani taron gaggawa kan halin da ake ciki a yankin na Gaza.
Masana dai na gargadin yiwuwar yakin ya iya zama mafi tsayi tsakanin bangarorin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu