Isa ga babban shafi

Sojojin Isra'ila na dab da yi wa yankin Gaza kawanya

Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant, ya bai wa jami’n tsaron kasar umarnin yi wa baki daya yankin zirin Gaza kawanya, a daidai lokacin da sojojin ke kai farmaki kan yankin Falasdinawa ta jiragen yaki.

 Jami’n tsaron Isra'ila za su yi wa baki daya yankin zirin Gaza kawanya.
Jami’n tsaron Isra'ila za su yi wa baki daya yankin zirin Gaza kawanya. REUTERS - AMIR COHEN
Talla

A cikin wani sakon Video da ya fitar, ya ce za su dakatar da komai a yankin na Gaza kama daga abinci da ruwa da gas da kuma wutar lantarki.

Wannan dai na zuwa ne bayan da kasar Austria ta sanar da dakatar da kai kayan agaji ga Falasdinawa, sakamakon harin da Hamas ta kai Isra’ila a karshen mako.

Ministan harkokin kasashen wajen kasar Alexander Schallenberg, ya ce za su yi bitar duk wani aiki da su ke gudanarwa a yankin Falasdinawa, sannan kuma su tattauna da kungiyar Tarayyar Turai da sauran kasashe kan lamarin.

Mutane ne da dama ne dai suka mutu a rikicin da ya barke, domin a cewar kakakin wata kungiyar bada agaji a Isra’ila Moti Bukjin, kimanin mutane 250 ne mayakan Hamas suka kashe a wajen wani bikin kalankuwan wakoki a kusa da Gaza.

Mutane ne da dama ne dai suka mutu a rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Hamas.
Mutane ne da dama ne dai suka mutu a rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Hamas. REUTERS - ITAI RON

Sakamakon irin asarar rayukan da aka yi, a lokacin zaman makon karshe na kwamitin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya a yau Litinin, sai da mahalarta taron suka mike tare da yin shuru na wani lokaci, don girmama wadanda suka rasa rayukansu a tsakanin Isra’ila da Gaza, kamar yadda wakiliyar Amurka a wajen taron Michele Taylor ta bukata.

Sashin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya ce sama da mutane dubu dari da 23 ne suka bar gidajensu a yankin Gaza, don tsira da rayuwarsu, sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a matsayin martani kan Hamas.

Sashin ya ce daga cikin wancan adadi, dubu 73 na Falasdinawan da ke gudun hijira, a cikin makarantu suka samu mafaka na wucin gadi.

Sama da Falasdinawa dubu dari da 20 suka tsere daga gidajensu a yankin Gaza.
Sama da Falasdinawa dubu dari da 20 suka tsere daga gidajensu a yankin Gaza. AFP - MOHAMMED ABED

Kasashe da dama sun fara kwashe mutanensu da suka makale a Isra’ila, sakamakon rikicin.

Ministan tsaron Poland Mariusz Blaszczak, ya ce rukunin farko na ‘yan kasar 120 sun isa gida a safiyar yau Litinin, bayan da wani jirgin sojin kasar ya kwasosu, ya yin da da ake dakon isar wasu jirage biyu dauke da ‘yan kasar da ke makale a a tashar jiragen sama ta Isra’ila.

Tuni dai kasashe da dama suka tashi tsaye don neman hanyar warware rikicin, inda a ranar Litinin din nan akaji Rasha da kungiyar kasashen Larabawa na kokarin samar da hanyoyin da za a warwari rikicin na Isra'ila da Falasdinawa.

A lokacin wata ziyara da shugaban kungiyar Ahmed Aboul Gheit ya kaiwa ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya ce su yi kokarin kare ci gaba da zubda jinin da ake yi tsakanin bangarorin biyu.

Kungiyar kasashen Larabawa na kokarin samar da hanyoyin da za a warwari rikicin na Isra'ila da Falasdinawa.
Kungiyar kasashen Larabawa na kokarin samar da hanyoyin da za a warwari rikicin na Isra'ila da Falasdinawa. AP - Amr Nabil

Wannan kuwa na zuwa ne a lokacin da kungiyar Tarayyar Turai ta kira taron gaggawa na ministocin kasashen wajenta don tattauna batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.