Isa ga babban shafi

Harin Isra'ila ba zai dakatar da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ba- Haneyah

Jagoran Hamas Isma’il Haniyeh ya bayyana cewa kisan ‘ya’ya da jikokinsa da Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai jiya Laraba ana tsaka da shagulgulan Sallah ba zai hana ko kuma dakatar da tattaunawar da yanzu haka ake yi don tsagaita wuta a Gaza ba, dai dai lokacin da ko a safiyar yau Isra’ilan ta ci gaba da kai hari yankin na Gaza da ke karkashin kawanya tsawon watanni.

Jagoran kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh.
Jagoran kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh. AFP - -
Talla

A jiya kadai Isra’ilan ta kashe mutanen da yawansu ya haura 120 amma duk da haka al’ummar yankin sun gudanar da sallolin idi har a masallacin Baitil Maqadis.

Harin Isra’ila a jiya ya kashe iyalan gidan Haniyeh da suka kunshi ‘ya’yanshi maza 3 da kuma jikokinshi 4.

Akwai dai bayanan da ke cewa kisan iyalan na Haniyeh wani yunkuri ne da Isra’ila ke yi don tunzura Hamas wajen ficewa daga tattaunawar da ake tsaka da yi, dai dai lokacin da kasashen Duniya ke matsa lamba ga kasar ta yahudawa.

Harin dai ya zo ne a dai dai lokacin da tattauna ke tsaka da gudana a birnin Alqahira na Masar a kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta wadda aka yi fatan yi tun a farkon watan Ramadana, da nufin sakin fursunonin bangarorin biyu da ke tsare.

A zantawarsa da kafar talabijin ta Aljazeera, Isma’il Haniyeh ya ce ko shakka babu Isra’ila na son tunzura Hamas ne don ta hakura da tattaunawar, amma su sani cewa sam harin ba zai sanya su dakatawa da tattaunawar ba.

Hamas dai yanzu haka na nazartar tayin tsagaita wutar da Amurka ta shiga tsakani wajen mika mata, sai dai wasu bayani da kafar talabijin ta CNN ta wallafa sun ce kungiyar ba ta da wadatattun fursunonin da za ta yi musaya da su don tsagaita wutar a yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.