Isa ga babban shafi

An cika watanni shida da barkewar yakin Isra'ila da Hamas a Gaza

Yakin Isra’ila da Hamas ya shiga wata na bakwai da barkewa a Zirin Gaza, a yayin da masu shiga tsakani ke ta kokarin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

Daya daga cikin tankokin yakin Isra'ila a Gaza. 4 ga Afrilu, 2024.
Daya daga cikin tankokin yakin Isra'ila a Gaza. 4 ga Afrilu, 2024. AP - Leo Correa
Talla

A halin yanzu dai an cigaba da tattaunawar neman cimma tsagaita wutar a Alkahira babban birnin kasar Masar, wanda ke samun halartar Fira Ministan Qatar da shugaban hukumar leken asirin Amurka ta CIA, sai dai akwai shakku kan ko manyan jami’an gwamnatin Isra’ila sun halarci zaman tattaunawar.

Wannan na zuwa ne a yayin da alaka ke neman yin tsami tsaknain Isra’ila da manyan kawayenta da suka hada da Amurka da wasu kasashen yammacin Turai, kan kisan da sojojinta suka yi wa wasu jami’an agaji bakwai a gaza, a yayin da suke tsaka da gudanar da ayyukansu.

Ya zuwa yanzu Falasdinawa sama da dubu 33,000 sojojin Isra’ila suka kashe a Gaza, tun bayan harin da mayakan Hamas suka kai tare da kashe Yahudawa dubu 1,170 a ranar 7 ga  watan Oktoban shekarar bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.