Isa ga babban shafi

An gano wani makeken kabari dauke da gawarwakin Falasdinawa a Khan Younis

A na cigaba da gudanar da ayyukan agaji domin zakulo gawarwaki  50 na wasu Falasdinawa da aka binne a wani makeken kabari, wanda aka gano a asibitin Nasser dake birnin Khan Younis.

Yayin zagulo wasu gawarwaki a Khan Younis
Yayin zagulo wasu gawarwaki a Khan Younis AP - Mohammed Dahman
Talla

An dai gano wannan kabari ne makonni biyu da janyewar  dakarun Israila daga birnin.

Ko a baya bayan nan daga cikin mutanen da Israila ta kashe a wani kazamin hari da ta kai birnin Rafa, akwai wata mata mai juna biyu da ‘ya’yanta 6, saidai likitoci sun yi nasarar ceto jaririn da ke cikin cikin mahaifiyarsa da rai.

Ma’aikatar lafiyar Falasdinu ta ce dakarun Isra’ila sun kashe akalla mutane 14 a wani samame da suka kai sansanin ‘yan gudun hijirar Nur Shams, su ka kuma kashe wani matukin motar kai dauki, daidai lokacin da yake kokarin kai ga wasu Faladinawan da suka jikkata a kudancin Nablus.

A halin yanzu da yakin Isra’ila ke cin karenta babu babbaka a Gaza, ta ke kuma neman kustawa Iran, Majalisar Wakilan Amurka ta amince da ba ta tallafin dala biliyan 26.

Tun bayan barkewar yaki a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, akalla Falasdinawa dubu 34,049 ne Isra’ila ta kashe, wasu dubu 76,901 kuma suka jikkata. Yayin da a nata bangaren mutane dubu 1,139 suka, an kuma rike Isra’ilawa da dama a matsayin fursunoni a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.