Isra'ila ta janye dubban sojojinta daga kudancin Zirin Gaza
Rahotanni daga Zirin Gaza na cewa dubban sojojin Isra’ila sun janye daga kudancin yankin na Falasdinu, ciki har da birnin Khan Younis, inda suka shafe watanni suna fafatawa da mayakan Hamas.
Wallafawa ranar:
Matakin na zuwa a yayin da aka cika watanni 6 da barkewar yaki a yankin na Gaza.
Sai dai wani mai fashin baki kan sha’anin tsaro a Isra’ilar ya ce janye sojojin da ta yi daga kudancin na Gaza ba ya nufin kawo karshen yakinta da Hamas ko kuma kusantar hakan, illa kawai dabarar sauya salon yakin.
A wani labarin kuma dubban ‘yan Isra’ila sun gudanar da zanga-zangar neman Fira Ministan kasar Benjamin Netanyahu yayi murabus, bisa zarginsa da gazawa wajen kare muradunsu.
Masu zanga-zangar sun kuma nemi a gaggauta kulla yarjejeniyar sulhun da za ta kai ga sako ragowar Yahudawan da mayakan Hamas ke garkuwa da su a Zirin Gaza.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu