Isa ga babban shafi

Isra’ila ta sanar shirin buɗe iyakokin kai agaji Gaza na wucin gadi

Isra’ila ta sanar cewa zata bude wasu iyakokin Gaza domin bada damar kai kayan agaji arewacin yankin na wucin gadi, sakamakon matsin lamba daga kasashe daban daban ciki harda babbar kawarta Amurka.

Thủ tướng Israel Natanyahu.
Thủ tướng Israel Natanyahu. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan gargadin da shugaban Amurka Joe Biden ya yi wa kasar a tattaunawar da suka yi da Firaminista Benjamin Netanyahu ta waya, inda ya bukaci gaggauta tsagaita wuta a hare haren da kasar  ke kaiwa Gaza da kuma bude kofofin kai kayan agajin, ko kuma Amurka ta sake matsayin manufofin ta a kan kasar.

A tattaunawa da suka yi yammacin jiya ta tsawon mintuna 30 Shugaba Biden ya shaidawa Netanyahu cewa manufofin Amurka akan Isra’ila sun dogara ne ga kare rayukan fararen hula da na ma’aikatan kai agaji a Gaza, a dai dai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsin lamba dangane da kashe ma’aikatan agaji guda 7 ‘yan kasashen Birtaniya, Canada da Australia.

Bayan da Isra’ila ta sanar cewa zata bude kofofin kai kayan agaji yankin Gaza, kasar Jamus tace Isra’ilan bata da wasu dalilai da zasu sa ta jinkirta bude kokfofin domin ganin kayayyakin da fararen hula ke bukata sun kai ga mabukata.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ne ta bayyana hakan yau Juma’a a shafinta na X.

‘‘Al’ummar Gaza suna bukatar ko wanne irin taimako a yanzu, saboda haka muna tsammanin gwamnatin Isra’ila zata gaggauta aiwatar da bude kofofin kai agajin’’. In ji Baerbock.

A ranar Juma’ar nan ne hukumar kare hakkin Bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya tace yanzu haka tana tara hujjoji da suke nuna Isra’ila a matsayin mai aikata laifuffukan yaki da kuma take hakkin Dan-Adam a yankin Zirin Gaza.

Ita dai Isra’ilar ta bayyana matsayin na hukumar majalisar dinkin duniyar a matsayin soki burutsu kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.