Isa ga babban shafi

Faransa ta yi tir da harin Sojin Isra'ila kan jami'an agaji a Gaza

Faransa ta yi ala wadai da harin Isra’ila kan motar jami’an agaji na kungiyar World Kitchen Centre da ya kai ga kisan jami’an agajin 7 lokacin da suke kan hanyarsu ta shigar da tallafin abinci yankin Gaza da al’ummarsa ke fama da matsananciyar yunwa.

Jami'an agajin World Kitchen Centre da Isra'ila ta kashe a Gaza.
Jami'an agajin World Kitchen Centre da Isra'ila ta kashe a Gaza. AP - Abdel Kareem Hana
Talla

Yayin wata ganawar ministan harkokin wajen Faransa Stéphane Séjourné da takwaransa na Amurka Antony Blinken da ta gudana a Paris, manyan jami'an diflomasiyyar biyu sun jaddada bukatar goyon bayan kasashen yamma ga Ukraine a yakin ta da Rasha.

A zantawar manyan jami'an diflomasiyyar biyu na Faransa da Amurka gaban manema labarai sun bukaci Isra’ila ta dauki alhakin harin wanda ya kashe jami’an agajin bakwai ciki har da ɗan Amurka da ɗan Canada da kuma ɗan Birtaniya baya ga ɗan Australia da Poland sai kuma Bafalastine guda.

Tuni dai Isra’ila ta bayyana harin da kuskure tare da shan alwashin yin taka-tsan-tsan a hare-haren da ta ke kaiwa.

Wannan kira na Séjourné da Blinken na zuwa a dai dai lokacin da bankin duniya ke kiyasin asarar da Isra’ila ta haddasawa yankin na Gaza zuwa dala biliyan 58 sakamakon yadda kasar ta Yahudu ta rushe kusan dukkanin gine-ginen zirin Gaza da Rafah.

Zantawar jami’an biyu ta kuma tabo batun yakin Rasha da Ukraine inda Faransa ta bukaci Turai ta sanya takunkumi kan kamfanonin Rasha da ke yaɗa labaran ƙarya.

Faransa dai na cikin manyan kasashen da ke samar da taimakon soji ga Ukraine da ke fuskantar karancin makamai da dakaru yayin da take kokarin dakile hare-haren Rasha.

Amurka ta kasance kan gaba wajen goyon bayan Ukraine a yakin da ta ke yi, sai dai Majalisar kasar ta toshe wani kunshin dala biliyan 60 da gwamnatin Biden ya shiya bai wa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.