Isa ga babban shafi

Faransa da Jordan da Masar sun yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a Gaza

Ministocin harkokin kasashen wajen Faransa da Masar da kuma Jordan sun yi kira da a gaggauta tsagaita wuta na dindindin a Gaza da kuma sako dukkan mutanen da ke hannun mayakan Falasdinawa.

Wasu Falasdinawa ke jiran karban abinci. 13/03/24
Wasu Falasdinawa ke jiran karban abinci. 13/03/24 REUTERS - Mohammed Salem
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jirgin ruwa na biyu dauke da kayan agaji zuwa yankin Gaza da yaki ya daidaita ya tashi daga kasar Cyprus, sama da makwanni biyu tun bayan da kayayyaki agaji na karshe ya isa yankin Falasdinu ta tekuru.

A halin da ake ciki Iyalan yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a Gaza sun yi kira da a gudanar da wani gagarumin gangami a gaban majalisar dokokin kasar a mako mai zuwa a daidai lokacin da suka samu goyon bayan dubban mutane da suka hallara birnin Tel Aviv ranar Asabar.

Shira Elbag, wadda mayakan Hamas suka yi garkuwa da ‘yarta Liri mai shekaru 19 a harin da aka kai Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ta yi wani roko mai tsotsa rai inda ta bukaci ‘yan kasar Isra’ila da su kara matsawa Firanminista Benjamin Netanyahu lamba.

"Lokaci ya yi da za mu fita yaki da halin ko in kula da rayuwa da gwamnatin Netanyahu ke nunawa," in ji ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.