Isa ga babban shafi

An sake tashi baram-baram a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

Tawagar wakilan Hamas da ke cikin tattaunawar yarjejeniyar tsagaita wuta a luguden wutar da Isra’ila ke yi a Gaza sun bar birnin Alqahira na Masar bayan gaza cimma jituwa tsakanin bangarorin da ke cikin tattaunawar, wanda ke nuna yiwuwar a iya fara azumin watan Ramadan ba tare da nasarar tsagaita wutar ba.

Isra'ila na ci gaba da kisan Falasdinawa a Gaza.
Isra'ila na ci gaba da kisan Falasdinawa a Gaza. © Amir Cohen / Reuters
Talla

Manyan kasashe ciki har da Amurka na fatan tsagaita wuta a hare-haren na Isra’ila gabanin kamawar watan Ramadana, sai dai tashi baram-baram a tattaunawar birnin Cairo ya sanya fargabar yiwuwar hare-haren na Isra’ila su ci gaba har zuwa cikin watan mai alfarma, musamman lura da yadda Firaminista Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da zafafa hari a Rafah.

Ma’aikatar lafiyar yankin Gaza ta ce alkaluman mutanen da Isra’ila ta kashe ya kai dubu 30 da 800 ciki har da wasu 38 da aka kashe cikin kasa da as’o’i 24.

A bangare guda Isra’ilan ta yi maraba da matakin kungiyar EU da ta amince da bude kafar shigar da kayan agaji yankin Gaza ta Cyprus bayan da Ursula von der Leyen ke cewa kafar za ta kasance a bude daga karshen makon nan don kange barazanar cutar yunwa a yankin mai fama da yaki.

Sai dai a bangare guda Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Isra’ilan game da yunkurinta na ci gaba da mamaya a yankin Falasdinawa inda shugaban hukumar kare hakkin dan adam na Majalisar Volker Turk ke cewa duk wani makamancin yunkurin kai tsaye zai kasance cikin laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.