Manyan motoci dauke da kayayyakin agaji sun shiga Gaza a karon farko
Rukunin farko na manyan motocin dakon kaya dauke da kayayyakin agaji ya shiga yankin Zirin Gaza wanda ke fama da hare-haren Isra’ila ta mashigar Rafah daga Masar a Asabar din nan.
Wallafawa ranar:
Wannan ne karon farko da motoci masu dauke da kayayyakin agaji suka shiga Gaza tun da wannan yaki ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas, mai mulkin Gaza, sama da makwanni biyu da suka wuce.
Kasashen duniya sun fara tsokaci a game da wannan al’amari na kokarin isar da agaji ga wannan yanki da yaki ya daidaita, inda shugaban hukumar kula da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce yana da kwarin gwiwar cewa wannan ne masomin ci gaba da shigar da kayayyakin agaji ga al’ummar Gaza.
Mashigar Rafah dai ita ce hanya daya tilo ta shiga Zirin Gaza, wadda ba a hannun Isra’ila take ba, kuma kasar ta Yahudawa ce ta amince a shigar da agaji ta hanyar, biyo bayan bukatar hakan daga babbar aminiyarta, Amurka.
Isra’ila tana luguden wuta a kan Zirin Gaza tun bayan harin da mayakan Hamas suka shammace ta da shi a ranar 7 ga watan Oktoba; hakan ya sa Isra’ilar ta ayyana yi wa yankin kawanya, inda ta yanke wutar lantarki da ruwa da makamashi.
Tun daga lokacin da aka fara kai wadannan hare-haren, sama da Falasdinawa dubu 4 da dari 1 ne suka mutu, akasarin su fararen hula, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Hamas ta sanar.
An rufe wannan mashiga ta Rafah bayan da wadannan motocin dakon kaya 20 suka wuce da kayayyakin agaji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu