Isa ga babban shafi
RIKICIN GAZA

Iran ta bukaci kasashen Musulmi su sanya wa Isra'ila takunkumi

Kasar Iran ta ce, membobin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya kamata su kakaba wa Isra'ila takunkumin man fetur da sauran takunkumai tare da korar dukkanin jakadun kasar, domin ta hakan ne za su tir da mummunan harin da aka kai a asibitin Al-Ahli Arab da ke Gaza.

Shugaban Iran, Ibrahim Ra'isi, yayin wata ganawa da jagoran kungiyar Hamas, Isma'il Haniyeh tare da tawagarsa a birnin Tehran, ranar 20 ga watan Yuni, 2023.
Shugaban Iran, Ibrahim Ra'isi, yayin wata ganawa da jagoran kungiyar Hamas, Isma'il Haniyeh tare da tawagarsa a birnin Tehran, ranar 20 ga watan Yuni, 2023. AFP - -
Talla

Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, gabanin taron kasashen kungiyar OIC da zai gudana a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, domin tattaunawa kan rikicin Isra’ila da Falasdinu.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi kira da a gaggauta sanyawa Isra'ila cikakken takunkumi daga kasashen musulmi da suka hada da takunkumin mai, baya ga korar jakadun Isra'ila da kuma yanke alaka da gwamnatin Yahudawan sahyoniyya.

Amirabdollahian ya kuma yi kira da a kafa wata tawaga ta lauyoyin Musulunci da za ta rubuta laifukan yaki da Isra'ila ta aikata a Gaza.

Kasar Iran dai ba ta da alaka ta diflomasiya da gwamnatin Isra'ila.

A daren ranar Talata, wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a wani asibiti a Gaza, ya kashe mutane kusan 500, abin da ya kasance, daya daga cikin hare-hare mafi muni tun fara tashin hankalin ranar 7 ga watan Oktoba.

Zanga-zangar goyon bayan Falasdinu ta barke a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka bayan harin da aka kai a Gaza, inda magoya bayan Falasdinu ke dandazo zuwa ofisoshin jakadancin Isra'ila a Jordan da Turkiyya da kuma kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke Lebanon.

An kuma gudanar da zanga-zangar a Iran, Morocco, Tunisia, Yemen da Iraki.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya soke ganawar da zai yi da takwaransa na Amurka, yana mai cewa harin da aka kai a  asibitin wani mummunan kisan kiyashi ne da Isra'ila ta aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.