Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kashe kimanin mutane 500 a asibitin Gaza

Daruwan mutane ne suka rasa rayukansu a wannan Talatar, sanadiyyar farmaki ta sama da Isra’ila ta kai kan yankin Gaza na Falasdinu, kuma mafi yawan hare-haren an kai su ne a kan wani asibiti da ke kula da wadanda suka samu raunuka a wannan yaki. 

Gawarwakin mutanen da harin Isra'ila ya kashe a asibitin Ahli Arab da ke Gaza.
Gawarwakin mutanen da harin Isra'ila ya kashe a asibitin Ahli Arab da ke Gaza. AFP - DAWOOD NEMER
Talla

 

Alkaluma daga majiyoyin kiwon lafiya a Gaza, sun ce adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon farmakin da Isra’ila ta kai a ranar Talata kawai ya kama daga 300 zuwa 500. 

An dai kai wadannan hare-hare ta sama ne a kan asibitin al-Ahli da ke Gaza, inda dubban fararen hula suka samu mafaka, yayin da wasu ke jinya ko kuma kula da majinyata da suka jikkata a tsawon kwanaki kusan 12 da aka share ana wannan rikici. 

Wasu bayanai kuwa sun ce, ko baya ga wannan asibiti, ruwan bama-baman da Isra’ila ta yi sun shafi wata makaranta mallakin Majalisar Dinkin Duniya, inda dubban mutane ke zaune a matsayin ‘yan gudun hijira, inda a can ma aka ruwaito cewa an samu asarar rayuka. 

Da aka nemi jin ta bakinsa a game da wadannan hare-hare, mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila Daniel Hagara ya ce ba ya da tabbas idan har an kashe wannan adadi, amma za su yi bincike a kai. 

To sai dai shugaban ofishin UNRWA da ke kula da ayyukan jinkai a Falasdinu, Philippe Lazzarini, ya ce ko baya ga hari kan makaranta mallakinsu, an kuma kashe mutane 6 a sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.