Isa ga babban shafi

Amurka na shirin ba da tallafin dala biliyan 95 ga ƙasashen Ukraine da Isra’ila da Taiwan

Amurka ta sanar da ware akalla dala biliyan 90 a matsayin gudumawa ta bangaren tsaro ga ƙasashe Ukraine da Isra’ila da kuma Taiwan. 

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden © Evan Vucci / AP
Talla

Amurka ta sanar da ware akalla dala biliyan 95 a matsayin gudumawa ta bangaren tsaro ga ƙasashe Ukraine da Isra’ila da kuma Taiwan. 

Matakin ya biyo bayan gagarumar rinjayen da yan jam’iyyar Damocrat suka samu a kan 'yan Republican a zauren Majalisar Wakilan ƙasar. 

Ana sa ran a cikin mako mai zuwa Biden ya sa hannu na amincewa da yin amfani da kudurin dokar ayyukan agaji. 

Daga cikin kudin za a ware wa Ukraine dala biliyan 60 da miliyan 840, sannan za a yi amfani da dala biliyan 23 wajen mayar da wasu makaman Amurka da aka yi hasararsu, hade da wasu kayayi masu muhimmanci, an kuma ware wa Isra’ila dala biliyan 26, da kuma dala biliyan 9 da miliyan 100 ga ayyukan jin kai a Isra’ilan, kana dala biliyan 8 da miliyan 120 zuwa ga ƙasashen da ke yankin Pacific, cikinsu har da Taiwan. 

Tuni dai Shugaban Ukraine Volodimir Zelensky ya mika sakon godiya ga Biden,  ya na mai yaba wa ƴan Majalisar bisa daukar wannan mataki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.