Isa ga babban shafi

Alkalan Birtaniya sun hura wa firaministan kasar wuta saboda Gaza

Wasu tsoffin alkalan Kotun Kolin Birtaniya sun bi sahun sama da mambobi 600 na kungiyar lauyoyuin kasar wajen kira ga gwamnati da ta dakatar da sayar wa Isra’ila makamai, inda suka ce, hakan ka iya shafa wa kasar kashin kaji a kisan-kare dangi a Gaza.

Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak a zauren Majalisar Dokokin Kasar.
Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak a zauren Majalisar Dokokin Kasar. AP - Jessica Taylor
Talla

Alkalan sun kanbama kiraye-kirayen da sauran lauyoyi da ƴan adawa ke yi na ganin firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ya sauya matsayarsa.

Tun bayan mutuwar wasu ma’aikatan agaji bakwai da suka hada da ƴan asalin Birtaniya uku a Gaza sakamakon wani kazamin harin Isra’ila, mista Sunak ke ci gaba da shan matsin lamba.

A cikin wata wasika mai shafuka 17 da alkalan da lauyoyuin suka rubuta, sun bayyana cewa, bai wa Isra’ila taimakon makaman soji da sauran kayayyakin yaki, ka iya sa a dauki Birtaniya a matsayin wadda ke da hannu a kisan kare-dangi da kuma wadda ke karan-tsaye ga dokokin jin-kai na kasa da kasa.

Kodayake firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana bacin-ransa kan yadda ake zargin sa da kisan kiyashin, yana mai cewa, kasarsa na mutunta dokokin kasa da kasa.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya musanta cewa, suna aikata kisan kare-dangi a Gaza.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya musanta cewa, suna aikata kisan kare-dangi a Gaza. © Ronen Zvulun / Reuters

Birtaniya dai ta sayar wa Isra’ila  wasu ƴan bama-bamai da manyan bindigogi da jiragen yaki.

Lauyoyin na Birtaniya sun tunatar da matsayar Kotun Duniya da ta umarrci Isra’ila da ta daina aikata duk wata ta’asa da za a iya bayyana ta a matsayin kisan kare-dangi, gami da jefa al’umma cikin yunwa.

Sai dai firaminista Sunak ya yi biris da kiraye-kirayen gaggauta dakatar da sayar wa Isra’ila makaman, yana mai cewa, gwamnatinsa na da kyakkyawan tsarin lasisi da za ta ci gaba da mutuntawa.

Kasashe sun yi wa Isra'ila caa bayan harin da ta kaiwa jami'an bada agaji

Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashe da kungiyoyin bada agaji, na ci gaba da Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai wa tawagar wata kungiyar bada agajin abinci ta Amurka ta World Central Kitchen, da ya yi sanadiyar mutuwar jami’anta 7 a Gaza.

Jami’in kula harkokin kasashen waje na kungiyar Tarayar Turai Josep Borrell, ya ce duk da bukatar bai wa fararen hula da jami’an bada agaji kariyar da aka yi, har yanzu ana ci gaba da asarar rayukansu.

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a harin na jiya Litinin, akwai ‘yan kasashen Australia da Birtaniya da Poland da wani da ke dauke da takardar zama dan kasashen Amurka da Canada sai kuma Bafalasdine.

A view of a vehicle where employees from the World Central Kitchen (WCK), including foreigners, were killed in an Israeli airstrike, according to the NGO as the Israeli military said it was conducting
Motar agajin da Isra'ila ta kaddamar wa hari a Gaza. REUTERS - Ahmed Zakot

A cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar Tsaron Amurka Adrienne Watson ta fitar, ta ce fadar White House ta kadu da harin da aka kaiwa jami’an bada agaji, don haka ta ce dole ne a bai wa masu irin wannan aiki kariya da kuma bada damar isar da kayan abinci.

Firaministan Australia Anthony Albanese, ya yi Allah wadan da wannan hari, inda ita kuma Poland ta rubutawa Isra’ila wasakar da ke cewar hare-harenta sun saba wa dokokin bada agaji na duniya.

Kasashen Birtaniya da Spain da Masar da Belgaum da Cyprus da Iran da Jordan da Scotland da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da sauransu, sun bukaci a gudanar da bincike kan lamarin da suka bayyana a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Tuni dai kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila Daniel Hagari ya fidda wani sakon bidiyo, inda yake jajantawa kasashen da suka rasa ‘yan kasarsu a wannan hari.

Duk da cewa bai fito fili ya bayyana cewar su ne suka dauki alhakin kai harin ba, ya tabbatar da cewar za su gudanar da bincike don kaucewa sake faruwar hakan a nan gaba.

Kungiyar bada agaji ta Red Crescent ta Falasdinu, ta ce za a dauki gawarwanin mutanen zuwa asibitin Abu Youssef al-Najjar da ke Rafah na Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.