Isa ga babban shafi

NATO ta yi Allah wadai da harin ramukon gayyar da Iran ta kai a Isra'ila

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi tur da ramukon gayyar da Iran ta yi akan Isara'ila bayan da ta kai mata hari a ofishin jakadan ta da ke Damascus na kasar Syria.

Ảnh do quân đội Iran công bố ngày 19/01/2024: Một tên lửa đạn đạo được phóng đi trong cuộc tập trận ở phía nam Iran.
Ảnh do quân đội Iran công bố ngày 19/01/2024: Một tên lửa đạn đạo được phóng đi trong cuộc tập trận ở phía nam Iran. AP
Talla

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi Alla wadai da harin da Iran ta kai a cikin dare a kan Isra'ila, tare da yin kira na ganin an kiyayi ci gaba da kai hare-haren domin gujewa bazuwar yankin.

Kungiyar tsaron ta NATO ta tir da wannan harin da Iran ta yi cikin dare tare da bayyana cewa tana ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa domin daukar matakan da suka dace.

mai magana da yawun kungiyar tsaron ta NATO Farah Dakhlallah ya ci gaba da cewa yana da matukar muhimmanci a kiyaye domin rikicin na iya dagula lamuran Gabas ta Tsakiya wanda hakan na barazana ga zaman lafiyar duniya.

Sai dai Iran ta yi barazanar duk kasar da t aba da sararin samaniyarta wajen kai mata hari to zata dandana kudarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.