Iran ta harba makamai masu linzami 16 yayin atasayen gargadi ga Isra'ila
Iran ta harba makamai masu linzami da dama a ranar Juma'a, rana ta karshe da ta gudanar da atasayen soji da ta shafe kwanaki 5 tana yi.
Wallafawa ranar:
Manyan hafsoshin sojin kasar ta Iran dai sun bayyana atasayen a matsayin gargadi ga babbar abokiyar gabarsu Isra'ila.
Babban Hafsan sojojin Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri, ya shaidawa gidan talabijin na kasar cewa, an tsara jerin atasayen ne domin mayar da martani ga barazanar da gwamnatin Isra’ila ta yi musu a baya bayan nan.
Janar Bagheri ya ce makamai masu linzami 16 da suka harba, kadan ne daga cikin daruruwan makamai masu linzami da Iran ta mallaka, wadanda za su iya amfani da su wajen kai hari kan dukkanin kasar da ta kuskura ta kai musu farmaki.
Sai dai, a wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ta yi Allah wadai da harba makamai masu linzamin da Iran ta yi, tana mai cewa hakan barazana ce ga tsaron yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu