Isa ga babban shafi

Isra'ila ta baiwa sojojinta umarnin fitar da fafaren hula daga Rafah kafin fara luguden wuta

Prime ministan Isra’ila Benjamin Natenyahu ya umarci sojojin kasar su fara aikin kwashe fararen hula daga yankin Rafah kafin fara kutsa kai da kuma luguen wuta a cikin sa.

Natenyahu na bayar da wannan umarni ne, dai-dai lokacin da yake fuskantar zanga-zangar adawa daga 'yan kasar
Natenyahu na bayar da wannan umarni ne, dai-dai lokacin da yake fuskantar zanga-zangar adawa daga 'yan kasar REUTERS - RONEN ZVULUN
Talla

Yankin a yanzu haka shine mafi yawan mutane a zirin Gaza.

Sanarwar na zuwa ne bayan shan chachaka daga kasashen duniya cikin kuwa har da Amurka kan yunkurinsa na kutsawa Rafah mai tarin Jama’a.

 

Majalisar dinkin duniya ta ce yanzu haka akwai mutanen akalla miliyan 1 da dubu 400 a yankin na Rafah da ke zama ko dai da ‘yan uwa ko kuma a sansanonin gudun hijira.

 

Sai dai kuma Isra’ila ta dage kan cewa Rafah ne waje na karshe da ke zama mafakar mayakan Hamas yanzu haka tun bayan da suka tserezuwa can a saboda luguden wutar da ke faruwa a Gaza.

 

Ta ce kokarin kaucewa illata fararen hular a barín wutar da take shirin yi a Rafah ne zai sanya ta fara kwashe su cikin gaggawa zuwa wasu yankunan da ke da aminci.

 

Sai dai kuma masu sanya idanu kan yadda yakin ke tafiya na ganin cewa yanzu haka babu wani waje da za’a kira shi mai aminci a kafatanin zirin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.