Isa ga babban shafi

Isra'ila na kulla makarkashiya don kawo karshen hukumar mu- Shugaban hukumar UNRWA

Hukumar bada agaji da taimakon gagagwa ta majalisar dinkin duniya ta zargi Isra’ila da yunkuri kawo karshen ta, kamar yadda shugaban hukumar Philippe Lazzarini ya shaida yayin tattaunawar sa da manema labarai yau asabar.

Philippe Lazzarini, Shugaban hukumar bayar da agaji ta majalisar dinkin duniya
Philippe Lazzarini, Shugaban hukumar bayar da agaji ta majalisar dinkin duniya © Johanna Geron / Reuters
Talla

Lazzarini ya bada misali kan yadda Isra’la ke ta kiraye-kirayen ya sauka daga mukamin sa a matsayin wata hanya ta kawo karshen hukumar.

Shugaban, yayin tattaunawar sa da gidan jaridar Tamedia da ke kasar Switzerland, ya ce binciken sirri ya nuna musu yadda kasar ke kai gwauro tana kai mari kawai don ganin ta kassara ayyukan hukumar ta yadda zai bata damar kisan fararen hula a Gaza ba tare da wata kungiya na kai musu dauki ba.

A cewar sa wannan wata daddiyar ajandar siyasa ce, wadda aka fake da rikicin Gaza wajen cimmata, sai dai yace matukar yana jagorantar hukumar ‘yan gudun hijirar Falasdinu zasu cigaba da samun tallafin da ya kamata komin rinsti.

Lazzarini ya ci gaba da cewa misalin hakan shine yadda kasar ke ci gaba da barna a Gaza, duk kuwa da cewa kungiyoyi na shige da fice wajen tallafawa fararen hula, shin menene zai faru idan babu irin wadannan kungiyoyi.

Ya ce koda janyewar da kasashe suka yi daga baiwa hukumar tallafi makarkashiya ce ta Isra’ila, wadda kuma ba zata yi tasirin komai ba, sai ma yiwa kasar Illa matukar bata yi taka tsan-tsan ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.