Isa ga babban shafi

Isra'ila ta ce za ta ci gaba da yaki da Hamas ko babu goyon bayan wata kasa

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Eli Cohen ya ce za a ci gaba da yaki da kasar ke yi a kan Hamas a yankin Zirin Gaza ko da goyon bayan kasashen duniya ko babu.

Fira Minitsan Isra'ila, Benyamin Netanyahu.
Fira Minitsan Isra'ila, Benyamin Netanyahu. © Abir Sultan / AP
Talla

Sanarwar tasa na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya caccaki yadda Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a ba kakkautawa a kan Zirin Gaza, a matsayin martani ga harin ranar 7 ga watan Oktoba  da Hamas ta kai mata.

A ranar Laraba kawayen Isra’ila sun zafafa matsin lamba a kanta sakamakon wannan yakin da ta ke yi da Hamas, inda ma Amurka da kanta ta bayyana hare-haren a matsayin na kan mai-uwa-da- wabi.

Ko a ranar Talata sai da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani  kudiri na neman tsagaita wuta, lamarin da ya ta’azzara matsin lamba a kan Isra’ila da Amurka.

Ya zuwa yanzu adadin wadanda suka mutu a wannan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza tun bayan harin 7 ga watan Oktoba ya zarce dubu 18, kuma har yanzu tana ci gaba da hare-hare, duk da bukatar Amurka ta sara ana duban bakin gatari.

Mahukuntan yankin Falasdinu sun ce samamen da Isra’ila ta fara a garin Jenin tun a ranar Talata da ta gabata ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.