Isa ga babban shafi

Kungiyar G-7 na nazarin yadda za a kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya

Ministocin harkokin wajen kasashen G7 na gudanar da taro kan yadda za a kawo karshen yakin da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma tashin hankalin da ya kunno kai a yankin gabas ta tsakiya.

Taron na da nufin lalubo mafita kan rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Taron na da nufin lalubo mafita kan rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. © AfricaNews
Talla

Tattaunawar da aka fara ranar Laraba a tsibirin Capri na Italiya, an shirya ta ne da nufin karfafa hadin gwiwar kasashen kungiyar ta G-7 da kungiyar AU, lamarin da gwamnatin Italiya ta ce tana kan tattaunawa da takwararta ta Amurka a kai.

Yayin da shugabannin kungiyar EU ke tattaunawa kan batun kara kakaba takunkumi kan Iran, ba a san matsayin kungiyar ta AU ba dangane da muhawarar da ake yi game da martanin Isra’ila kan harin da Iran ta kai mata.

Har yanzu dai kasashen Afirka basu nuna goyon bayan harin na Iran ko kuma karkatawa ga goyon bayan Isra’ila da ikirarin da take yin a ramuwar gayya ba.

Duk da haka masana sun lura cewa Kungiyar AU bata goyon bayan duk wani takunkumi da aka shirya kakabawa Iran ko kuma wata kasa ba.

A kodayaushe kungiyar na magana kan bukatar dage takunkumin da kasashen yamma suka kakaba wa Zimbabwe, Cuba da sauran kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.