Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya za ta koma zama kan bukatar samar da kasar Falasdinu

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da shirin gudanar da zama na musamman a makon nan don tattaunawa tare da kada kuri’a kan bukatar samar da kasar Falasdinu baya sanya kasar a sahun cikakkin mambobin zauren majalisar, kudirin da tun fil azal ke fuskantar tirjiya daga Amurka.

Wani zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Wani zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. AFP - CHARLY TRIBALLEAU
Talla

Zaman wanda Majalisar Dinkin Duniyar ta tsara gudanarwa a yammacin gobe Juma’ar, matsin lamba daga wasu kasashen Larabawa ya tilasta dawo da shi zuwa yau Alhamis dai dai lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar ke gudanar da taro na musamman kan bukatar mahukuntan yankin  na Falasdinu da ke neman kujera a kwamitin.

Tun a shekarar 2011 jagoran na Falasdinawa Mahmoud Abbas ya mikawa Majalisar bukatar ‘yantar da yankin na Falasdinu don kasancewa kasa mai cin gashin kanta kamar yadda makiyiyarta Isra’ila ta ke, sai dai tun a wancan lokaci Amurka da kawayenta sun hau kujerar naki game da kudirin.

Kudirin dai na bukatar amincewar akalla mambobi 9 cikin 15 da ke cikin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniyar gabanin iya sahale bukatar samar da kasar da Falasdinu mai cikakken ‘yanci.

A baya-bayan nan kiraye-kirayen bukatar samar da kasar ta Falasdinu ya taso gadan-gadan bayan da Isra’ila ta kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 33 a hare-haren tsawon watanni 6 da ta shafe ta na kaiwa sassan Gaza tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.