Isa ga babban shafi

Netanyahu ya zargi Hamas da dakile kokarin rage mutuwar fararen hula a Gaza

Fira Minista Benjamin Netanyahu, ya ce duk wani kokari da dakarun Isra’ila ke yi wajen takaita adadin rayukan fararen hular da ke salwanta a Zirin Gaza, inda ya dora alhakin gazawar kan mayakan Hamas da ya nanata cewar suna amfani da fararen hula a matsayin garkuwa. 

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kenan.
O primeiro-ministro israelense, Benjamin Netanyahu, fala durante a cerimônia de abertura da Agência de Promoção de Comércio e Investimento do Ministério do Brasil em Jerusalém, em 15 de dezembro de 2019. AFP - GIL COHEN-MAGEN
Talla

Kalaman Fira Ministan na Isra’ila dai sun zo ne a daidai lokacin da dakarun kasar ke ci gaba da kai samame zuwa cikin asibitoci a Zirin Gaza, musamman na Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a yankin na Falasdinu, inda Isra’ila da Amurka suka dage kan cewar mayakan Hamas na amfani da shi a matsayin mafakar karkashin kasa. 

Bayan kwanakin da suka shafe suna bincike a asibitin na Al Shifa da wasunsa dai, har yanzu Isra’ilar da Amurka basu gabatar da wata kwakkwarar shaidar da ke tabbbatar da  zargin da suke yi ba. 

Hare-haren dakarun Isra’ila da kuma yadda suke afka wa asibitoci a Gaza dai na ci gaba da fusata kasashe da dama da sauran hukumomin agajo, inda a Dazun nan shugaban hukumar lafiya ta Duniya Tedros Adhanom ya bayyana cewar bai ga amfanin Majalisar Dinkin Duniya ba, muddin ta gaza dakatar da barnar da Isra’ila ke yi a yankin Falasdinawa. 

A Amurka kuwa, an yi arrangama ne tsakanin masu zanga-zangar nuna kin jinin Isra’ila da ‘yan sanda a babar gadar birnin San Fransisco da ke karbar taron tattalin arziki tsakanin wakilan kasashen Asia da Pacific. 

A Jamus kuwa, da yammacin wannan Juma’a shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya isa Berlin, inda zai gana da shugabannin kasar kan yakin Zirin Gaza, musamman m akan bukatar tsagaita wuta da kuma wasu muhimman batutuwa na kasa da kasa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.