Isa ga babban shafi

Kasashen duniya na caccakar Isra'ila saboda kai hari asibiti

Samamen da dakarun Isra’ila suka kaddamar a baya-bayan nan ta hanyar kutsawa cikin asibitin Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a Zirin Gaza, ya janyo wa kasar caccaka gami da yin Allah-wadai daga kasashe, da sauran hukumomin kasa da kasa suka ce, matakin Isra'ila ya wuce gona da iri. 

Wasu daga cikin sojojin Isra'ila.
Wasu daga cikin sojojin Isra'ila. REUTERS - ALEXANDER ERMOCHENKO
Talla

Bayan bayyana kaduwa da kutsen dakarun Isra’ilar, Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya kuma koka kan rashin tabbas din tsaron rayukan ma’aikatan lafiya da marasa lafiyar da ke cikin asibitin na Al Shifa, wadanda ya ce an katse duk wata hanyar sadarwa tsakaninsu. 

Shi kuwa shugaban ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths cewa ya yi ya zama dole sojojin Isra’ila su fifita kare jarirai, da marasa lafiya da sauran ma’aikatan lafiya sama da bukatar da ta sanya su kaddamar da samame a cikin babban asibitin. 

A nata martanin Amurka cewa ta yi ba ta  goyon bayan kai wa duk wani asibiti farmaki, lura da cewar baya  ga ma’aikatan jinya da masu jinyar, wuri ne da fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ke samun mafaka a Zirin Gaza. 

Sai dai kungiyar Hamas ta yi fatali da kalaman na Amurka, wadda ta zarga da hada baki da Firaminista Benjamin Netanyahu wajen yada karyar cewa mayakanta na amfani da asibitin Al Shifa a matsayin sansani, farfagandar da Hamas din ta ce za ta bai wa sojojin mamaya damar yi wa karin Falasdinawa kisan kiyashi. 

Isra’ila da ke shan caccaka kuwa, kare kanta ta yi da cewa samamen da ta kaddamar farautar mayakan Hamas ne da take zargin sun mayar da asibitin na Al Shifa sansani, amma ba da niyyar cutar da fararen hula ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.