Isa ga babban shafi

Harin Isra'ila ya kashe mutane 80 a makarantar Al-Fakhura dake Gaza

Duniya – Kungiyar Hamas tace wasu kazaman hare haren da Isra’ila ta kai sansanin ‘yan gudun hijirar dake Jabalia sun yi sanadiyar hallaka mutane sama da 80 a yau asabar.

Yankin Khan Younes dake Gaza
Yankin Khan Younes dake Gaza REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya yace akalla mutane 50 suka mutu sakamakon harin da Isra’ila ta kai yau da asuba a makarantar Al-Fakhura dake cikin sansanin wanda ke karkashin Majalisar dinkin duniya, abinda ya haifar da suka daga kwamishinan jinkai na Majalisar.

Sansanin 'yan gudun hijirar Jabalia
Sansanin 'yan gudun hijirar Jabalia REUTERS - STRINGER

Jami’an Majalisar dinkin duniya sun ce dubban mutanen da suka rasa matsugunansu ne suka samu mafaka a cikin makarantar da Isra’ila ta kai harin, abinda ya sa shugaban jinkai na Majalisar Martin Griffiths ya yi Allah wadai da harin, wanda yace ya ritsa da mata da yara da kuma maza.

Griffiths yace sansanin mastuguni ne na samun mafaka, yayin da kuma makarantar wuri ne na samun ilimi, saboda haka babu dalilin da zai sa a kaiwa fararen hula hari, musamman wadanda suka samu mafaka.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana cewar hotunan wadanda harin ya ritsa da su sun mamaye kafofin sada zumunta, cikin su harda wadanda ke kwance a kasa jina jina, duk da yake bai iya tantance sahihnacinsu ba.

Sansanin ‘yan gudun hijirar Jabalia ne mafi girma a arewacin Gaza, wanda ke dauke da Falasdinawa sama da miliyan guda da rabi wadanda yakin da ya barke na makwanni 6 ya raba da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.