Sojojin Isra'ila sun bada sa'a guda ga kowa ya fice daga asibitin al-Shifa
Dakarun Isra’ila sun umurci llikitoci da marasa lafiya daa ma wadanda yakin da ake yi ya daidaita so fita daga asibitin al-Shifa, inda suka ba su sa’a da su yi haka su na mai tilasta su da bakin bindiga su bi umurnin nasu, kamar yadda majiyoyi daga asibitin suka bayyana.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Amma aa wani sako da ta wallafa a shafintaa na dandalin sada zumunta na X, wanda aka sani da Twitter kafin yanzu, rundunar sojin Isra’ilar ta musanta tilasta wa wani barin wannan asibitin, tana mai cewa sojojinta sun karbi bukatar da shugaban asibitin ya mika musu ne ta cewa su bari wadanda ke bukatar ficewa daga asibitin su fita.
Sai dai shugaban hukumar da ke kula da asibitoci a Zirin Gaza, Mohammed Zaqout, ya jaddada cewa sojin Isra’ila ne suka tilasta musu barin asibitin da bakin bindiga.
Mutane sama da dubu 7 ne ke cikin wannan asibiti, cikinsu har da marasa lafiya da suka hada da jarirai, wadanda ke halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, tun bayan da dakarun Isra’ila suka yi wa asibitin.
Tun da farko wani likita a asibitin al-Shifa ya ce ba zai yiwu a fice daga asibitin ba, amma daga baya rahotanni sun ce an fara ffitar da mutane daga asibitin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu