Isa ga babban shafi

Sojojin Isra'ila sun yi gumurzu gaba da gaba da mayakan Hamas

Sojojin Isra’ila da mayakan Hamas sun yi arangama gaba-da-gaba kuma kusa da kusa a Zirin Gaza a wannan Alhamis, yayin da suka shafe tsawon sa’o’i 10 suna gumurzu, inda Isra’ila ke cewa, ta yi nasarar tarwatsa wani sansanin mayakan na Hamas.

Wasu daga cikin sojojin Isra'ila da ke yaki da Hamas a Gaza
Wasu daga cikin sojojin Isra'ila da ke yaki da Hamas a Gaza AFP - JALAA MAREY
Talla

Mayakan  Hamas dauke da makaman roka da manyan bindigogi sun fafata da sojojin na Isra’ila ne da ke cikin motocin yaki masu sulke a can yankin arewacin Zirin Gaza da buraguzai suka mamaye.

Bangarorin biyu sun fafata ta sama da ta kasa, yayin da Isra’ila ke cewa ta gano wata tungar mayakan Hamas ta karkashin kasa da suke amfani da ita wajen kitsa kaddamar da hari.

A cewar Isra’ila, an kashe gomman mayakan na Hamas a gumurzun, amma a bangarenta, jumullar sojoji 34 kadai ta rasa ya zuwa yanzu a cewarta.

Wasu daga cikin mayakan Hamas a Gaza.
Wasu daga cikin mayakan Hamas a Gaza. ASSOCIATED PRESS - MOHAMMAD BALLAS

A yanzu dai, karyayyun bishiyoyi da lalatattun allunan titi da kuma lankwasassun fitilun hanya, na cikin abubuwan da ake iya gani a yankin na arewacin Gaza yaki da yaki ya daidaita.

Isra’ila ta kafa tutocinta kan wasu gina-gine da ke gabar teku a arewacin na Gaza, sannan babu wata alamar motsin dan Adam a wurin sakamakon yadda yakin ya tilasta wa dubban daruruwan mutane tserewa.

A bangare guda, asibitocin birnin Gaza na cikin mawuyacin hali, kama daga rashin wadatattun kayan aiki a daidai lokacin da dimbin gawarwaki ke jibge kan tituna da wasu wurare, baya ga gawarwakin da aka sanya su makare a cikin motoci masu firinji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.