Isa ga babban shafi

'Yan sandan Madagascar sun tarwatsa taron 'yan adawa da barkonon tsohuwa

'Yan sandan kasar Madagascar, sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a wurin taron ‘yan adawa da magoya bayansu, wadanda ke neman mukamai a zaben shugaban kasar da aka shirya gudanarwa a farkon watan Nuwamba, a wani dandalin dake tsakiyar babban birnin kasar.

Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Marc Ravalomanana yayin artabu da jami'an tsaron da suka harba hayaki mai sa hawaye a wani gangami da ya gudana a Antananarivo, ranar 2 ga watan Janairun 2019.
Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Marc Ravalomanana yayin artabu da jami'an tsaron da suka harba hayaki mai sa hawaye a wani gangami da ya gudana a Antananarivo, ranar 2 ga watan Janairun 2019. © Mamyrael, AFP
Talla

A ranar 9 ga watan Nuwamba ne al'ummar kasar za su kada kuri'a domin zaben shugaban kasa da gwamnoni.

An shafe makonni da dama ana shirye-shiryen babban zaben kasar da ke tsibirin Tekun Indiya a cikin wani yanayi mai cike da fargaba.

'Yan takara 11 ciki har da tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana, sun yi kira da a gudanar da wani gangami da sanyin safiyar ranar Litinin, a Place du 13 Mai, wurin da ake amfani da shi wajen baje kolin takaddamar siyasa a Madagascar.

Da dama daga cikin ‘yan takarar, sun isa wurin taron kafin lokacin da aka sanar, wato karfe 09:00 na safiya agogon GMT, inda ‘yan sanda suka nufi wurin tare da jefa musu barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.

A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP, masu tsaron lafiyar tsohon shugaban kasar, Ravalomanana,  sun yi gaggawar boye shi a wani sashe na dandalin, bayan da aka harba hayaki ma isa hawayen.

Hukumomin kasar sun ce, ba a sahalewa ‘yan adawa gudanar da taron ba, abin da ya sanya aka tura daruruwan jami’an tsaro zuwa harabar da sanyin safiya.

‘Yan takara 13 ke neman kujerar shugabancin kasar, ciki har da shugaba mai ci Andry Rajoelina mai shekaru 49, wanda aka zaba a shekarar 2018, abin da ya kawo karshen mulkin Marc Ravalomanana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.