Isa ga babban shafi

Kakkarfar guguwar Freddy ta yi mummunar barna a Madagascar

Zuwa mutane 4 suka mutu a Madagascar, bayan da guguwar Freddy ta afka wa yankunan gabar ruwa da ke gabashin kasar a daren jiya, cikin gudun kilomita 130 a Sa’a 1. 

Kakkarfar guguwar Freddy.
Kakkarfar guguwar Freddy. VIA REUTERS - NASA
Talla

Rahotanni sun ce wani matashi mai shekaru 27 ya mutu sakamakon nutsewa cikin ruwa, tun ma kafin guguwar ta kammala yin karfi a arewacin yankin Mananjary da ta afkawa a gabashin Madagascar, baya ga wasu mutum 3 na daban da guguwar ta kashe, lamarin da ya haifar da fargabar fuskantar karin hasarar rayuka da dukiya. 

Tuni dai aka rufe makarantu, kasuwanni da sauran ma’aikatun gwamnati a larduna 4 daga cikin 6 da kwararru suka ce guguwar za ta ratsa.  

A shekarar bara ma dai garin Mananjary mai yawan mutane dubu 25 dake gabar teku, na cikin yankunan Madagascar da guguwar Batsirai  ta yi wa barna, inda ta kashe mutane fiye da 130. 

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta yi hasashen cewa fiye da mutane miliyan 2 da dubu 300 guguwar Freddy za ta shafa a bana, domin kuwa daga Madagascar guguwar za ta afkawa yankunan kasashen Mozambique da Zimbabwe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.