Isa ga babban shafi

Kakkarfar guguwar Cheneso ta kashe mutane 38 a Madagascar

Mahukuntan Madagascar sun tabbatar da yadda kakkarfar guguwar Cheneso mai tafe hade da ruwan sama mai karfi da ta afkawa yankunan kasar ta yi sanadin mutuwar mutane kusan 30 baya ga rushe tarin gidaje, lamarin da ya kara yawan mutanen da ibtila'in ya shafa.

Wani yanki da kakkarfar guguwa ta afkawa a Madagascar.
Wani yanki da kakkarfar guguwa ta afkawa a Madagascar. © Viviane Rakotoarivony, AP
Talla

Tun a makon jiya ne kakkarfar guguwar Cheneso ta afkawa yankunan kasar, sai dai a jiya lahadin bannar da ta ke yi ta mumama inda hukumar kula bala'o'i ta bayyana cewa zuwa yanzu guguwar ta raba mutane akalla dubu 38 da muhallan su yayin da ta shafi mutane dubu 83,181.  

Bayanai sun ce guguwar wadda ke gudun kilomita 116 zuwa 118 a sa'a guda, ta taho da ruwan sama mai karfin da ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa, makamanciyar wadda ta faru a watan Nuwaban bara. 

A watan Afrilu da ya gabata zuwa Nuwambar bara kasar ta sha fama da ibtila'in guguwa mai karfi wadda ta hallaka mutane kusan 100 ta kuma lalata gidajen sama da dubu 700. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.