Isa ga babban shafi

Madagascar: Ambaliya ta wanke gidaje 700 bayan mahaukaciyar guguwa

Mahaukaciyar guguwar da ta afka wa garin Sambawa na Madagascar na ci gaba da barna, bayan ambaliyar Ruwan da guguwar ta haddasa wadda ta shafe garin baki daya. 

Wani gida da guguwa ta lalata a Manajary, Madagascar.
Wani gida da guguwa ta lalata a Manajary, Madagascar. © Viviene Rakotoarivony/AP
Talla

Bayanai sun ce tun ranar Juma’a da guguwar da aka yiwa take da Chabeso ta fara har kawo yanzu garin na Sambawa na karkashin ruwa saboda ambaliyar da ta faru. 

Ma’aikatar jin kadi da takaita aukuwar ibtila’i ta kasar ta tabbatar da batan mutum guda, sannan sama da mutane 300 sun bar garin, yayin da gidaje fiye da 700 suka rushe. 

Wannan ce mahaukaciyar guguwa ta farko a kakar 2022-23, waddac aka saba yi daga watan Oktoba zuwa Afrilu. 

An ci gaba da zabga ruwan sama kamar da bakibb kwarya, amma ana ganin gugwar na raguwa ainun. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.