Adadin mutanen da guguwar Batsirai ta kashe a Madagascar ya kai 92
Adadin mutanen da mahaukaciyar guguwar da aka yiwa suna Batsirai ta kasha a kasar Madagascar ya kai 92, yayin da kungiyoyin agaji ke ci gaba da kokarin taimakawa mutane sama da 110,000 dake bukatar agajin gaggawa.
Wallafawa ranar:
Ofishin agajin gaggawa a kasar yace adadin mutanen da suka mutu a Yankin Ikongo inda matsalar tafi girma ya kai 71, yayin da mutane sama da 61,000 suka rasa matsugunin su.
Wani dan majalisar da ya fito daga yankin Brunelle Razafintsiandrofa yace akasarin mutanen sun mutu ne sakamakon rushewar da gidajen su suka yi akan su.
Majalisar Dinkin Duniya tare da kungiyoyin agajin sun fara kai kayan agaji ga mutanen da hadarin ya ritsa da su.
Kasar Faransa ta tura jami’an agajin ta 60 domin taimakawa wajen samar da tsaftacaccen ruwan sha a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu