Isa ga babban shafi
Madagascar - Yunwa

Mutane dubu 400 na cikin hatsarin shiga bala'in yunwa a kudancin Madagascar

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya WFP, ta ce yankin kudancin kasar Madagascar na fuskantar fari, wanda ke gaf da ingiza mutane akalla dubu 400 cikin bala’in yunwa.

Wasu mazauna yankin kudancin kasar Madagascar dake fama da karancin abinci.
Wasu mazauna yankin kudancin kasar Madagascar dake fama da karancin abinci. © WFP/Tsiory Andriantsoarana
Talla

Babbar dakatar hukumar samar da abinicin mai kula da kudancin Afrika Lola Castro ta yi gargadi ne a karshen makon nan yayin taron manema labarai, inda ta ce tuni bala’in farin ya halaka mutane da dama da suka hada da yara da manya a kudancin kasar ta Madagascar.

Castro ta bayyana halin da yankin na Kudancin Madagascan ke ciki a matsayin mafi muni da ta gani cikin shekaru 28 da ta shafe tana aiki, idan aka dauke yunwar da aka yi a yankin Bahr el-Gazal da a yanzu ke Sudan ta Kudu a shekarar 1998.

Tuni dai gwamnatin kasar ta Madagascar tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya suka kaddamar da gidauniyar neman tallafin dala miliyan 155 domin baiwa al’ummar kudancin Madagascan tallafin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.