Isa ga babban shafi
Madagascar

Yunwa ta tilasta wa al'ummar wasu yankunan Madagascar cin ganye da kwari

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta ce al’ummar kudancin Madagascar sun koma cin ganye da fari don magance yunwar da ta tsananta a yankunasu, biyo bayan mummunan fari.

maza na neman ruwa a busashen kogin Mandrare  a Madagascar.
maza na neman ruwa a busashen kogin Mandrare a Madagascar. AP - Laetitia Bezain
Talla

Wani babban jami’i a hukumar Amer Daoudi ya ce a halin da ake ciki, rayuwar yara kanana na cikin hatsari, musamman ma wadanda ke kasa da shekaru 5 da ba sa samun abinci mai gina jiki.

Da yake jawabi ga taron bita na maajalisar dinkin duniyaa Geneva ta bidiyto, Daoudi ya ce ya ga abin takaici a kauyukan da ya ziyarta, inda mutane suka koma cin wasu na’ukan ganyayyaki da kwarin  ba a saba ci ba.

Madagascar na daya daga cikin kasashen nahiyar Afrika da talauci ya yi kamari, kuma. rashin ababen more rayuwa da sauyin yaanayi ya jefa al’ummartda suka kai miliyan 26 cikin bala’i.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.