Isa ga babban shafi
Madagascar

Alkaluman mutanen da suka mutu a hadarin kwale-kwalen Madagascar ya kai 85

Mahukuntan Madagascar sun sanar da karuwar alkaluman mutanen da suka mutu a hadarin kwale-kwalen farkon makon nan zuwa 85 bayan gano karin gawarwaki 21 yau alhamis a ci gaba da laluben mutanen da suka bace a hadarin.

Hadarin kwale-kwale a kasar ta Madagascar da ke tsibirin Tekun India a gabashin Afrika ba sabon abu ba ne.
Hadarin kwale-kwale a kasar ta Madagascar da ke tsibirin Tekun India a gabashin Afrika ba sabon abu ba ne. © via Reuters/Madagascar Defence Ministry
Talla

Tun a litinin din da ta gabata ne kwale-kwalen dakon kayan dauke da mutane 138 ya kife a tsakar gabar tekun da ke arewa maso gabashin kasar ko da ya ke an yi nasarar tsamo mutane 50 da ransu a lokacin yayinda wasu kusan 80 suka bace.

A cewar shugaban rundunar 'yan sandan Madagascar da ke tabbatar da alkaluman ga manema labarai ya ce zuwa yanzu gawarwakin mutane 85 aka kai ga tsamowa.

Wasu bayanai na cewa jirgin kwale-kwalen wanda na dakon kaya ne bashi da izinin jigilar fasinja daga hukumomin kasar.

Mahukuntan Madagascar sun ce kwale-kwalen ya dauki mutanen da suka wuce kima wanda ya kai shi ga nutsewa yana tsaka da tafiya bisa ruwa.

Baya ga hadarin jirgin kwale-kwalen dai kwana guda tsakani Madagascar ta sake gamuwa da hadarin jirgin Shalkwafta wanda ke dauke da manyan jami'an gwamnati ciki har da ministan jinkai, wadanda suma suka fada ruwa ko da ya ke ministan ya tsira da ransa bayan ninkayar sa'o'i fiye da biyu a cikin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.