Isa ga babban shafi

Guguwar Freddy ta afkawa Mauritius tare da tunkarar Madagascar

An soke tashin jirage sama tare da rufe kasuwannin musayar hannayen jari a Mauritius, sakamakon kakkarfar guguwar da ta tunkaro kasa tun a ranar litinin, wadda ta haddasa ruwan sama kamar da bakin kwarya, iftila’in da akai hasashen zai sauka a kasar Madagascar cikin daren yau.

Yadda igiyar ruwa ta fara murdawa a yakin Belle Mare na kasar Mauritius sakamakon guguwar Freddy
Yadda igiyar ruwa ta fara murdawa a yakin Belle Mare na kasar Mauritius sakamakon guguwar Freddy Laura Edwards via REUTERS - LAURA EDWARDS
Talla

A halin da ake ciki dai babu wata ma’aikatar gwamnati da ke aiki, yayin da aka rufe shaguna, bankuna da gidajen mai tare da dakatar da zirga-zirgar jama'a, lamarin da ya sa kafa ta dauke daga kan tituna.

Da fari dai hukumar kula da yanayi ta Mauritius ta yi gargadin cewa gudun kakkarfar guguwar da aka yi wa lakabi da Freddy na iya kaiwa na kusan kilomita 280 cikin sa'a guda.

Sai dai bayanan karshe da hukumar ta fitar a daren ranar Litinin sun bayyana cewar, guguwar ta Freddy ta tunkari arewacin kasar Mauritius cikin gudun kilomita 120, ana kuma sa ran za ta kai yankunan Yammaci da Kudu maso Yammacin kasar cikin gudun kilomita 30 a sa’a daya.

A Madagascar da ke makwaftaka da Mauritius kuwa, masana sun yi hasashen cewa guguwar Freddy za ta afkawa sassan kasar ne a daren yau Talata.

Hukumar ta yi gargadin fuskantar ruwan sama mai karfi, yayin da guguwar za ta rika tsala gudun kilomita 250 a cikin sa'a guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.